GAME DA LITTATAFAMMU

MANNIR AHMAD ADAM GETSO SHAFIN HOTUNA ADIRESHIMMU WEBSITES MASU AMFANI SLIDE SHOW LITTATTAFAI DA HAND-OUT JARRABAWA LABARAI GUEST BOOK FEJIN SIYAYYA MENENE SABO? DABAI FILMS

LITTATTAFAN DA MUKA BUGA, DA WANDA ZAMU BUGA

INTRODUCTION TO INTERNET

BROWSING

EMAILING

CHATTING

SEARCHING ON THE INTERNET

MOBILE INTERNET

DUK MUN RUBUTA SU DA HAUSA NE

 

HAND-OUT DINMMU NA FARKO:- KOYI YADDA AKE SHIGA INTERNET

KOYI YADDA AKE SHIGA 

 (INTERNET)

 

GABATARWA

Da sunan Allah mai Rahama mai jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga manzommu Annabi Muhammad (SAW);

Bayan haka, na rubuta wannan Hand Out dinne domin yan uwa na hausawa irin wadanda basuda lokacin da zasuje Computer, su koyo yadda ake shiga Internet, Kuma suna matukar Sha’awan abin, amma basu da lokacin da zasuje su koyo, ko basu da wanda zai zauna ya koya musu, To saboda hakane na rubuta wanan hand Out din, Shi wannan wannan Hand Out din ko baka taba shiga Internet ba, in ka karanta shi daga farko harkarshe, to Insha Allahu Zaka iya shiga Internet harma kabudewa kanka sabon E-Mail Address.

Sannan a wannan Hand Out din nayi bayani gameda yadda ake shiga Internet daga cikin Handset, ko mutum bashi da lokacin da zaije cyber café yayi browsing to ko a’ina kake zaka iyayin browsing din  ta cikin Handset, yayi duk abin da zaiyi kamar yadda zaiyi a Computer.

Kuma na rubuta shine don ganin yadda zamanin yanzu komai sai kaji ance Internet ana ta abubuwa da dama a Internet amm a yawancin mutanemu basu sani ba,a yanzu hatta aikin Gwamnati zakaga ana nemashi ta Internet ake nemansa, ………

….. Domin Ayanzu zakaga mutum yana taneman aiki bai samu ba, amma yanzu idan ka shiga Internet akwai inda zakaje ka katambayi irin aikin da kakeso, ajero ma sunan kamfanunnuka ko ma’aikatar da take neman ma’aikata na wannan aikin alokacin sai dai kawai ka aika da wasika ……...

 

 

MENE INTERNET

Internet (Internetworking), wurine da ake zuwa a yi binciken wani abu urine da aka……….

Hada computer duniya wuri daya domin aikawa da sakonni na sauti, na magana, hoto da sauransu zuwa kowane wuri na duniya, harma aikawa da sakonni zuwa duniyar wata,  ………………………

 

TA YAYA AKA SAMO INTERNET

Internet ansamo shine bayan shekara 20 da suka wuce, samunshi ya samo asaline da wata hadakanya da majalisar tsaro ta amurucka da ake kira ARPAnet, Ita wanan ARPAnet an hada tane ta hanyar harhada computer wuri daya domin samun information a lokaci guda, sai har ya zamanto aka hada wannan network din da telephone line, yadda za’a iya aikawa da sakonnin ta daruruwan kilomitoci.

 

 

TA YAYA INTERNET TAKE AIKI

Internet yana aiki ne kamar wayar tafidagidanka, shima yana aiki ne da network wacce ake kira Intenet Service Provider (I S P), Shi Internet ta wurin aikawa da information yana amfani da wani abu wanda ake kira Internet Protocol shi Internet protocol shine yake nuna DATA (information) dinka zasu ko daga ina suke, misali idan zaka aika da wasika irin ta gargajiya bawai zakaje ka ajje wasikar a post office bane, a’a yana bukatar karubuta adireshin da wasikar zataje, to shima haka internet protocol yake a internet, yana da nambobi guda hudu, kumka kowace namba tana kasa da 256, nambobin suna nan kamar haka:- 192.112.36.5  ko  128.174.5.6     kaga nambobin farko suna nuna daga wane irin network sako yake, na dama daga karshe shike nuna daga wacce computa bayanin yafito,  misali:- kana kana cyber café a computer ta 12 sannan network din su shine 128 kaga ip naka zai zama 128.xxx.xxxx.12

MENENE AMFANIN INTERNET

Internet bazan iya lissafo amfanin shi gabadayaba saboda afaninsa yana da matukar yawa amma ga kadan daga ciki:-

1. Ansamu mutane su 25 sun haddace Alkur’ani acikin wata shida ta cikin Internet.

2. Ansamu mutane fiye da miliyoyi sun zamo millionaire ta cikin Internet.

3. Ansamu mutane da dama sun kamala degree din su cikin sauki ta cikin Internet.

Ansamu mutane miliyoyi sun samu aiki, sana’o I ta cikin Internet.

ABUBUWAN DA AKE YI A INTERNET

 

1.        Bincike ta fanning ilimi mai zurfi, kamar su:-

Tarihin sahabbai, Tarihin yakukkunan da manzon Allah yayi, Tarihin ka’aba, Tarihin sauran kasashe, Tarihin Al’umma da yarensu da sauran abubuwa masu zurfi

Koyon karatu:-

2.        Akwai websites din dazakaje ana koyarma da karatu, har a rinka baku assignment, har in ka gama abaka certificate, idan kana son website duba feji na (send).

3.        Neman magani n wani ciwo:- idan wani ciwo na damunka akwai websites din dazakaje karubuta abin dayake damun ka, idan kayi sendin, zakaga an aikoma dasunayen  magungunan wanan ciwon

4.        Neman Aiki:- akwai website da dama dazaka shiga a Internet kanemi Aiki, kamar aikin Gwamnati, aikin typing kana zaune a gida, da sau ransu. Idan kana son list din websites din (send)

5.        Siyayya:- a internet akwai websites din da zaka rubuta abin da zaka siya a fadamaka farashin sa, in ma kana da credit card kasiya idan daga kasar waje ne ayoma shippin dinsa zuwa Nigeria a fada maka adireshin da zakaje ka karbi abin naka.

6.        Duba Taswira:- akwai websites da dama dazakaje karubuta sunan local government dinku ko kauyenku akawo ma map din kauyen gabadaya da hanyoyi duk, har wanda basan kauyen ba zaka iya nunamai hanyoin da zai je gidanku.

7.        Aikawa da sakonni da karban sakonni:- ta internet zaka iya aikawa da sakonni zuwa wurare dabam dabam, zaka iya aikawa da sako daga website zuwa handest.

SAURAN ABUBUWAN SUNE:-

8.        Kallon bidiyo:- kamar su msn, cnn da sauransu.

9.        Yin abokanai daga kasashen waje

10.     Yin magana da mutum yana ganin ka kana ganin sa.

 

INANE CYBER CAFÉ?

Cyber café wurine da aka tanada domin shiga Internet, wurine da zakaga computoci duk anyio connectin dinsu da internet, idan kaje wurin kana son kayi browsing zaka basu kudin awowin da kakeson kayi sai su baka wata takarda da take dauke da password din. Kaima zaka iya bude cyber café abune mai sauki (send).

 

MENE WEB BROWSER?

Web browser itace softwayar da zata baka damar shiga yanar gizo-gizo kayi browsing, misalin web browser sune:- Microsoft Internet Explorer, Opera, Netscafe Navigator, Mozilla, dasauransu.

 

ME AKE NUFI DA WEBSITE?

Website itace taron feji (page), wadanda suke dauke da bayanai (rubutu), hotuna, sauti, da abubuwa masu motsi, wanda ananne zakaje kakaranta bayanan dakake so misalin website sune:- www.bbchausa.com  .

 

MENE INTERNET ADDRESS?

Su Email address wasu abubuwane guda wato Email da www, su wadannan suna karkashin wani abune da ake kira domain name system, amfaninsa shine domin tantance adireshin yanargizo, a internet.

 

 

 

 

P3=BROWSING

BAYANI DAKI-DAKI GAME DA YADDA KAE SHIGA YANAR GIZO-GIZO

A wanan bangaren, zanyi bayanine akan yadda zaka shiga Internet kayi browsing da yadda zakayi amfani da mouse wurin yin browsing din, da fark bari nafara da mouse.

 

YADDA ZAKAYI AMFANI DA MOUSE

Shi mouse dashi ake amfani wurin motsa pointer din dake cikin monitor (screen din computer), shine zakaga kana motsashi itama pointer din na motsawa, kuma idan zaka rike mouse zaka rike shine kamar haka:-

=mfig30=

sanan Idande kana browsing idan zakayi click koyaushe karinka yin click din bangaren hagu, sannan idande kana cikin website bazakayi click din wuri ba sai kaga pointa din ta zama hoton hannu, duk inda kaga ta zama hoton hannu za’a iya shiga wurin, wato zaka iya click a wurin, sanan inda zakayi click din zai iya zamowa rubutu ko hoto ko abu me motsi, duk lokacin da kayi click akan abu zai bude ma wannan abun, misali:- ka bude website din www.bbchausa.com kana duba fejin sai kaga wani wuri an rubuta LABAUN SAFE  to dakaje kan tsakiyar rubutun zakaga pointar ta zama hannu, sai kayi click a wurin, to zai kaika shafin da aka kawo labarum safen, sannan kada kamanta koyaushe zakayi click karinka yin click din bangaren hagu na mouse din, sanan a wasu shafin zakakyi amfani da ENTER na kibod wurin yin click, kamar a yahoo sign in zaka iya yin amfani da ENTER wurin click din sign in din, kuma zaka iya yin amfani da mouse wurin yin sama da feji ko kasa, zakazo can barin karshe na screen zaka wani arrow asama da wani akasa saikazo kayin click akan aron zakaga fejin nayin sama ko kasa, idan kuma baka ganeba zaka iya amfani da aron sama ko na kasa ajikin kibod din.

Sanan yanzu zan koma inyi bayani daki-daki wurin shiga internet din.

 

1.NEMAN DAKUNAN SHIGA YANAR GIZO-GIZO (CYBER CAFÉ).

Da farko idan kanason kashiga internet zaka tafi inda cyber café take, wato inda zakaje kasamu mutane ana ta browsin kamar haka:-

=mfig01=

sanan idan garin dakake babu cyber café to zaka iya shiga Internet ta cikin Handset dinka zan yi bayani nan gaba.

 

3. YADDA AKE SHIGAR DA PASSWORD DIN ABUDE DESKTOP

Idan kaje cyber café zaka tambayi irin awar da kake so kayi yawnacin awa daya bata wuce N100, idan ka basu kudin zasu baka watya ‘yar takarda wacce password din yake cikin ta, bayan sun baka sai kazo ka samu computer da bakowa akai, zaka sameta kamar haka

=mfig02=

bayan kazo ka zauna, zak duba inda aka rubuta (misali click here to enter a password),zaka ga wurine da dogon layi kamar haka                              sai kazo cikin wurin kayi click sai ka kwafe password din awanan wurin ba yan ka kwafe sai kayi click din login, ko kadanna ENTER, kana Deanna nawa zata bude maka DESKTOP, kamar haka:-

=mfig03=

wanan shi ake kira desktop.

 

YADDA ZAKA BUDO  WEB-BROWSER KA SHIGA

Bayan ka budo desktop, sai kaduba inda aka rubuta daya daga cikin wadannan:-  Internet Explorer, Fire Fox, Opera, Netscape Navigator. Da kaga daya daga cikin wadannan sai kayi double click, idan bakaga ko wane ba sai kaje can kasa gefen hagu zaka ga inda ka rubuta START sai kaje wurin kayi click, bayan kayi click sai ka duba inda aka rubuta Internet Explorer,  sai kayi double click akan wurin, idan kuma baka ga kowanne ba sai ka tambayi masu lura da cyber café din.  Bayan kayi click akan Internet Explorer zakaga ta bude maka feji kamar haka:-

=mfig04=

Ms Internet Explorer ita ce web browser din da tafi sauki wurin shiga internet, kuma yawancin kowace cyber café kaje zaka samu suna da internet explorer, don haka ko yaushe kaje browsin sai ka duba internet explorer a desktop. Kuma ita internet explorer software ce, wani zai iya yin tambaya yace wai mene internet explorer ko mene software, kuma mutane da yawa suna mamakin wai tayaya computa take aiki, har im bakayi abu daidai ba tagyara maka, harma kaga tana maka gargadi, to kafin im baka amsar wadannan tambayoyi bari in dada fada maka wai menene computer kamar yadda na yi bayani a farko, to ita dai computa duk abin dakaga tanayi to wannan abin sa mata akayi, duk wani gargadiu dakaga tana yi to mutum ne yazauna ya shirya mata, wanan abin da ake shirya mata shi ake kira program,  sanan program din ake harhada wa ashirya mata akirasu Software, ko kaima zaka iya shirya computer program na Hausa, idan ka samata zakaga kowane abu da zata rinka nuna maka da hausa zakaga tana yi, har gargadi duk da hausa, tambaya ma da hausa. Akwai wani software da nashiray na hausa na yin maakin dalibai na makaranta, kana yin run din program din a computa, zaka ga ta tambayeka da hausa; kamar haka zata tambayeka maakin duka makarantar zakayi ko maakin wani aji zakayi?,  idan ka zabi na aji, sai ta kara tambayarka.. daliban ajin sunawane sannan darasi nawa kae koyarwa a ajin, idan ka shigar da wanan zata tambaye ka daga maaki nawane mutum za’a sa ya fadi sanan   tace shigar da maakin step by step sai ka danna enter, idan ka gama ka danna ENTER, zaka ga taware maka suanan kowa da maakin da yacoi da position din da ya zo, harma idan kana son kayi wa kowa report shiit zata yi maka, kai dai akinka shine shigar da maaki. To kaga wannan abin shi ake kira software, kuma akwai software dabam dabam danayi na hausa, idan kana so, zaka iya aiko da email zuwa  manniruahmad@yahoo.com  ko (send).To kaga anan Ms Internet Explorer shima software ne wanda kamfanin Microsoft takje shiryawa.

P4=OPEN NEW ACC.

YADDA AKE BUDE SABON E-MAIL ADDRESS

Bayan kaje cyber café, kasiya time ambaka password kashigar da password din ka budo internet explorer, (fml=START—INTERNET EXPLORER). Sai ka duba can sama kusa da inda akarubuta Address, sai kazo kayi click a wannan dogon layin, karubuta,  mail.yahoo.com  kamar haka:-

=mfig32=

bayan ka rubuta sai kadanna Go ko ENTER. Bayan kadanna enter zaka ta bude maka wani feji kamar haka:-

=mfig05=

 

HANYOYIN DA ZAKABI KABUDO FORM DIN REGISTAR E-MAIL NA YAHOO

Bayan yabudo maka fejin, sai ka duba inda aka rubuta sign up sai kayi click bayan kayi click sai kajira shi zai kawo maka form din yahoo registration, bayan ya kawo maka form din yahoo registration,

=mfig08=

YADDA AKE CIKE FORM DIN RIGISTAR YAHOO

yanzu sai kafara cike form din kamar haka:-

 

 

 

 

 

AIKAWA DA FORM DIN

Bayan ka kamala cike form din, sai kaduba inda aka rubuta I agree sai kayi click din wurin, bayan kayi click din zaka dan cira har compuatr ta gama reading din form din bayan ta gama bayan tagama in kayi dai dai zakaga ta kawo ma wani sabon feji an rubuta Registration is Complete. Kamar haka

=mfig15=

shi wanan fejin zaka iya yin printing dinsa, idan kana son kayi printin dinsa kira masu kula da cyber café din su yi maka printin din, in kuma zakayi dakanka sai kadanna FILE-PRINT.

KAMMALA REGISTER

Lokacin da ta nunama registration is complete, idan kaduba kasan zakaga an rubuta continue to yahoo mail, sai kayi click din wurin, idan kayi click din wurin, zakaga ya bude maka email din ka, zaka ga an rubuta eg=welcome sager.

 

 

P5=EMAILING

YADDA AKESHIGA E-MAIL

Shi E-Mail address zaka iya budeshi a wurare kamar haka  yahoo.com  hotmail.com  mail.com  lycos.com  netaddress.com  email.com  37.com. Kamar  yadda nayi bayani a baya, bayan kaje cyber café kaje harka budo internet explorer, zaka zo kusa da inda aka rubuta address, sai karabuta mail.yahoo.com bayan karubuta sai kadanna Go  za’a budo ma feji :-

=mfig32/2=

bayan fejin ya bude, sai kazo inda aka rubuta yahoo ID, anan sai karubuta email dinka ba dole bane sai kasa @yahoo.com, bayan ka rubuta sai kadanna TAB ajikin kibod, ko kayi click din inda aka rubuta password sai karubuta password dinka bayan karubuta sai kayi click akan Sign in   sai kajira yafude bayan yabude zakaga an ma Wellcome, idan kuma by bude ba to kayi mistake din wani harafi, sai kasake shigarwa.

=mfig11=

 

IDAN ZAKA KARANTA WASIKA

Idan zaka karanta wasika, sai kayi click akan inda aka rubuta inbox, ko kuma CHECK MAIL ko inda aka rubuta You have xx unread message, sai kayi click din wurin, bayan kayi click ta jero maka wasikun dakake dasu sai kazo, kan wasika, kan abin da wasikar ta kunsa sai kayi click, kana yin click zakaga wasikar ta bude sai ka karantata.

 

RUFE WASIKA BAYAN ANGAMA KARANTAWA

Bayan ka gama karanta wasika, idan zaka goge sai ka danna DELETE zaka ganshi a saman wasikar ko a kasan wasikan,in ka gama karantawa sai kadanna CHECK MAIL or INBOX.

 

IDAN ZAKA RUBUTA WASIKA

Lokacin daka bude email dinka, idan wasika zaka rubuta sai kazo sama bangaren hagu zaka ga inda akarubuta  COMPOSE sai kayi click bayan kayi click zai bude maka wani feji kamar haka:-

=mfig13=

Kara girman rubutu

Idan zaka rubuta wasika kana son ka kara girman rubutun, zaka duba sam kadan cikin inda kake rubuta wasikar, zakaga karamar A da babban A inkaje wurin kafin ka danna zakaga an rubuta Front Size sai kayi click din wurin, sai kazabi rin girman rubutun dakakeso.

Sa kala a rubutu

Idan kanason kasawa subutun dakake yi kala, zakaje jerin layin daka dauko na baya, inda kaga anyi wani T , kafin kayi click zakaga anrubuta text colour, sai kayi click din wurin, zai kawomaka kaloli sai kazaba kalan dakakeso kayi click.

Saka hyperlink a rubutu

Shi hyperlink rubutu ne, wanda idan kadanna rubutun zai kaika websites din da aka rubuta a jikin wannan hyperlink din, misali wani abokinka ne baisan ebsite din Google ba sai kana son ka aika masa da website din ta cikin email dinka, sai kazo jerin wurin da kadauko sauran zakaga inda akayi hoton kamar duniya da wani abu kamar akwa ajikin, kafin kayi click zakaga an rubuta create hyperlink sai kayi click din wurin, amma farko sai karubuta website din misali Google  (sai kayi highlight dinsa) bayan karubuta sai kasa mouse dinka a gaban G sai kadanne sai kaja harzuwa e  zakaga yai baki sai kaje wurin creat hypalink kayi click sai karubuta website din eg= www.google.com sai kadanna ok, duk acikin wasikar zakayi wannan.

 

Sa Attach File

Attach file ana sashine idan kanson ka aika da hoto ko wani file daga computer dinka, idan kanason ka aika da attach file lokacin daka budo wasika zakaga wani wuri anrubuta Attach files sai kayi click a wurin zai budo maka wani wuri sai kayi click akan browse bayan kayi click saika zabi file dinda zaka aika bayan kayi click akan file din sai kayi click akan open  sannan sai kayi click din attach files  sai kajirata ta gama loda file din sai kayi click akan continue message sai kaci gaba da wasikarka.

 

AJJE WASIKA A DRAFT

Idan kana rubuta wasika sai baka gamaba kuma kaga lokacin ka ya kusa karewa ko kana son ka ajje wasikar bayanzu zaka aika da itaba, zaka iya ajje ta a draft lokacin da kadawo kaci gaba da rubuta ta sannan sai ka aika, yada zaka ajje abu a draft shine, lokacin da kake rubuta wasika idan kaduba saman wasikar zakaga inda aka rubuta SAVE AS DRAFT to nan zakayi click sai ta ajje ma wasikar duk randa kazo sai kaci gaba.

 

IDAN ZAKA DAUKO WASIKA DAGA DRAFT KACI GABA DA RUBUTA TA

Duk lokacin daka zo kabude email dinka, idan zaka budo wasika daga DRAFT saika duba inda aka rubuta DRAFT sai kayi click din wurin bayan kayi click din wurin zaka ga anbudoma jerin wasikun daka ajje su a draft sai dai kawai kayi click akan wasika kaci gaba da rubutata.

 

AIKAWA DA WASIKA

Lokacin dakagama rubuta wasika gabadaya, sai kazo inda aka rubuta To:  sai ka rubuta adireshin wanda zaka aikawa da wasikar awurin, eg=  To:  manniruahmad@yahoo.com  idan kuma zaka aikawa da mutane da yawa sai ka rubuta email din na farko saikasa comma “  ,    misali zaka aikawa da mutum biyu mannirgetso@yahoo.com,sagir13131@yahoo.com haka zaka tajera sunayen email din kana raba su da kwama. Bayan ka gama rubutawa sai kaduba sama zaka ga inda aka rubuta SEND sai kayi click din wurin, idan wasikar ta tafi zata nunama Message Send ,

 

IN ZAKA GOGE WASIKA

Kamar yadda nayi bayani da farko I dan kana sonka goge wasika sai ka danna DELETE ko kayi check din wasikun da zaka goge wato kayi musu good (wani dan box zakagani lokacin da ka bude wasikunka dan wannan karamin box din sai kazo cikinsa kayi click ) , bayan kayi check din ko wane wasika sai kadanna DELETE zai goge maka wasikun dakayi check din nasu.

YADDA AKE NEMO WASIKA

Misali wani yaynka ya aiko ma da wasika  acikin wasikar ya aikoma da nambobin scratch card na NECO sai baka ga wasikar ba kuma shi yace ya turo ta, to lokacin daka budo E-MAIL din ka zakaga inda aka rubuta  SEARCH MAIL a hagu da wurin zakaga wani dogon box sai kayi click acikin sai ka rubuta NECO ko karubuta PIN bayan karubuta sai kayi click akan SEACH MAIL, in dai wasikar tana email dinka zaka ga ankawo ma ita, sai dai kawai kayi click akan wasikar ta bude.

 

 

P6=CHATTING

MENE CHATTING?

CHATTING wata hanyace dazukuyi magana da mutum ta hanyar rubuta wa juna sako, ta hanyar rubutu dakuma ta hanyar sauti da kuma gani, wato zaku iya magana da mutum kana ganin sa yana ganinka.

Kuma  shi chatting hanyace dazaka hadu da abokanai daga kasa shen waje. Kuma shi chattin amfi yawan yinsa ta hanyar rubuta wa mutumn sako, misali ka hadu da wani dan SAUDIYA sai ka rubuta mai assalamu alaikum, a lokacin shima zai rbuto ma, wa’a laikumussalam, a haka zaku yi ta magana dashi, idan yana da webcam zaka iya ganinsa, idan kaima kana da webcam zai iya ganinka,

 

ME AKEYI A CHATTING?

Abubuwan da akeyi a chattin suna dayawa, anayin kamar su:-

1.        Kasuwanci.

2.        Haduwa da Likitoci kana tambayarsu cututtuka suna baka sunayen magunguna na cututtukan.

3.        Haduwa da malamai (irin mallam saudiya) kana tambayarsu wasu abubuwa suna baka amsa.

4.        haduwa da Malamai na book.

5.        Haduwa da abokanai daga kasashe dabam dabam.

6.        Yin aiki (na cika form, typing da sauransu), ana biyanka.

7.        Mitin(kamar wata ma’aikata zata iya yin mitin idan ma’aikatan nata suna nesa da juna.

Da sauransu. Yawancin  abubwan da akeyi anayinsu ne ta hanyar aikawa da sakonni ta rubutu magana gani(webcam).

 

MENENE AMFANIN CHATTING?

-          Amfanin chatin ya na dayawa sosai domin tanan zaka iya koyan karatun haddar Alkur’ani mai girma.

-          kuma zaka iya haduwa da likitoci kana tambayarsu magungunan cututtuka suna baka amsa kamar yadda nayi bayani.

 

YADDA AKE SHIGA CHAT (YAHOO MESSENGER)

Shi chattinj dabam yake da E-Mail da Browsing, shi bayan kabudo desktop, maimakon kadanna Internet Explorer, shi sai dai kadanna YAHOO MESSENGER , zaka ganshi a nan desktop ko idan ka danna START—YAHOO MESSENGER, idan baka ganshiba sai ka tambayi masu kula da cyber café din, kuma shi double click zakayi akanshi(nb= duk lokacin dazakayi click akan yahoo messenger ko waninsa ka dena click akan rubutu akan hoton zaka rinka click), idan kayi double click akan Yahoo Messenger zai budo ma hoto kamar haka:-

=mfig17=

bayan ya budo maka, sai karubuta email dinka agaban inda akasa Yahoo ID, amma idan kazo rubuta emai din badole sai kasa @yahoo.com computer tasan at yahoo.com ne, bayan karubuta sai kadanna TAB a kibod, ko kasa mouse kayi click a gaban inda aka rubuta PASSWORD anan sai karubuta password dinka, kamar dai yadda kake shiga email, bayan kagama sai kadanna Sign in ko kadanna ENTER duk wanda kdanna daidai ne, bayan ka danna zaka hira ya bude maka, bayan ya bude maka kamar haka:-

=mfig19=

bayan yabude maka saika duba can sama inda aka rubuta MESENGER sai kayi click din wurin sannan kayi click din YAHOO CHAT  sannan JOIN A ROOM, idan baka gane ba to kaduba sama inda akayi wani abu kamar hoton handset da kan telephone akan layin idan kaduba bangaren dama zaka ga wani alamar arrow guda iyu kamar haka irin wannan guda biyu É, idan kaje kan arrow din sai kayi click bayan kayi click sai kayi click akan CHAT sai kajirashi yabude, in baibude ba sai kasake zuwa wurin wannan arrow din ka sake click.

 

YADDA ZAKA ZAFI CATEGORY DA ROOM KASHIGA

Bayan ya bude zaka ga ya budo maka wani wuri kamar haka:-

=mfig20=

zaka ga jerin CATEGORIES sai kazabi category din da zaka shiga sai kayi click (misali= SCHOOL & EDUCATION),  bayan kayi click zai sake jero maka jerin ROOMS anan ma sai ka zabi room din da zaka shiga (misali:- study group), bayan kayi click sai kadawo kasa zaka ga inda aka rubuta Go to Room sai kayi click, zakga yabudo maka wani feji zaka jira harwani dogon abu yacika bazai wuse sakan 10, sai kayi click akan Enter Chat .

 

YADDA ZAKA GA YAWAN MUTANEN DA SUKE CIKIN CHAT ROOM

Bayan kadanna ENTER CHAT zakaga an bude maka chatroom din kamar haka:-

=mfig21=

idan ka duba bangaren dama Email din wadanda suke cikin dakin ne.

Idan kaduba wadanda suke bangaren dama kuma zakaga wadansu kamarsunsa headphone wasu kuma kamar suna cikin tibi, wasu kuma ba komai.

Wadan da suke da abu kamar headphone zaka iya magana dasu, wato suna (voice chat).

Su kuma wadanda suke cikin tibi, zaka iya ganin su, wasu kuma har zaka iya ganinsu kayi magana dasu.

Idan kana son kaji bayanin yadda zaka iya ganinsu ko kayi magana da mutum (send).

 

YADDA AKE DUBA MUTANEN DASUKE CIKIN CHAT ROOM DA IRIN ABUBUWAN DA SUKE RUBUTOWA

Idan kaduba bangaren dama kuma, nan kuma zakana ganin rubutu na tafito wa (misali mannir: joint the room), wato anan nunama yanzu mannir ya shigo dakin chatin din, kuma anan ne zakaga kowan rubuto abin da yaga dama  (misali mannir: akwai wani bahaushe kuwa?), to kaga ananne idan kana son kayi wa mutum magana sai kaje kan emaildinsa kayi double click.

 

YADDA AKE TABO MUTUM A CHATTING

Abagaren dama zakaiya ganin wanda kasan email dinsa, ko wani wanda kake son kuyi cattin dashi, yanda zakayi shine kaje kan email din mutum a bangaren dama kayi click, sananna sai kayo kasa kayi click akan inda aka rubuta IM, bayan kayi click zaka ga wani window ya fito, to a wannan window din zaka rinka rubuta abinda zaka aika wa wancandin, misali zaka iya rubuta mai Hi sai kayi send ko kadanna ENTER.

 

YADDA AKEYIN CHATTING

Bayan kayi click akan ID din mutum, kuma kayi click akan IM, wani window ya fito kamar haka:-

=mfig22=

sai kazo nan kasa sai kayi click, sai karubuta Hi, sai kayi ESND ko kadanna ENTER, sai kajira kaga reply, yana dawo da reply zaka ga bottom toolbar yayi ja, sai kayi click din wurin. Reply din zaka iya ganin sager:Hi ko  asl?, idan kaga msl asl?, yana tambayarka shekarunka nawane sannan kai namijine ko mace sannan a wane gari kake, shine ma’anar asl, zan yi bayanin irinsu nan gaba, to ta haka zaku ta communication da mutum, idan kana son kayganshi saika (send).

 

WASU KALMOMIN CHATTING DA MA’ANONINSU

Akwai kalmomin da ake amfani da su a wurin chattin don rage dogon rubutu, misali:-

-          Name? = yaya suanan ka, Ko ya sunan ki.

-          Age? = shekarun ka/ki nawa.

-          Country? = a wace kasa aka haife ka/ki?.

-          Location? = a ina ka/ki ke yanzu.

-          Asl? = shekarun ka/ki nawa, na miji ne kai ko ke mace ce, a ina ka/ki ke yanzu?.

-          Asl plz? = don Allah shekarun ka/ki nawa, na miji ne kai ko ke  mace, a ina kaki ke yanzu.

-          M/f? = Namiji ne ko mace.

-          Dasauransu

A lokacin da kuka fara chattin da mutum zaka iya ganin ya rbuto maka:- asl?, wato yana nufin kai waye, namiji ne ko mace kuma shekarunka nawa, kuma a wace kasa ka ke ko kike. Akwai abubuwa da dama da ake rubutawa wurin chattin nan kadanne daga cikin su.

 

IDAN KAYI ABOKI ZAKA AJJE SHI A MESSINGER LIST

Idan kuna cattin da mutum sai kanason ka ajje shi a messenger list(wurin da zaka ajje email din mutane, yadda duk lokacin daka shiga yahoo messenger zaka iya gane mutum yana kan computer ko baya nan), lokacin da kuke chattin da mutum din idan ka duba saman dakin shi wannan mutum din zaka ga wani hot kamar kai anyi alamar Tarawa ajikin kan to nan zakazo kayi click, zaka ga ya bude maka, wani feji sai ka danna next har sau biyu na karshen sai kadanna Finish, bayan ka gama zakaga sunan email dinsa a jikin yahoo messenger dinka, kuma zaka iya zuwa da Email adireshin wani , ka ajje a messenger list, kamar yadda zanyi bayani nan gaba.

 

YADDA ZA’A AJJE E-MAIL DIN MUTANE A MESSENGER LIST

Zaka iya samun Email adireshin din abokinka ka ajje shi a messenger list yadda duk lokacin da kahau computer, zaka iya ganewa shima yana kan computa ne ko bayakai, misali kasamo email adireshin manniruahmad@yahoo.com  idan ka budo yahoo messenger sai kaduba inda akajera hoton su handsets da sauransu zaka ga wani abu Kaman kan mutum da alamar Tarawa ajikin abun, sai kayi click a wurin zai bude maka wani wuri, sai karubuta email adireshin bayan ka rubuta sai kadanna next harsau biyu daga karshe sai kadanna finish, zakaga email dinsa ya fito a cikin yahoo messenger dinka.

 

YADDA ZAKA GANE ABOKIN KA YANA KAN COMPUTER KO BAYANAN

Duk lokacin da kashiga yahoo messenger, idan ka ajje Email adireshin mutane a messenger list, to a farkon sunan kowa zakaga hoton wani abu kamar kan mutum, to duk kan dakaga yayi kala wato yayi kalar dorawa to wannan mai Email din yana kan computer wato yana cikin chattin, wadanda kuwa kaga basu da kala to basa kan computer, ta haka zaka iya gane aboinka yana kan computa ko bayanan, im ma bayanan zaka iya rubuta mai sako yadda duk lokacin da yahau kan computa zai ga wannan sakon.idan kana son karubuta wa mutum sako zaka je kan email adireshinne saikayi double click bayan kayi double clcik sai kajira ya budo maka wani kjaramin window bayan ya budo maka window din sai karubuta abin da zakarubuta sai kayi send.

 

YADDA ZAKUYI MAGANA DA MUTUM KANA GANIN SA YANA GANIN KA

(send)

(more info. Send email to mannirgetso@yahoo.com).

 

P7=SEARCH

YADDA ZAKA BINCIKO BAYANAI TA CIKIN INTERNET

A wanna shafin zanyi bayani ne akan yadda zaka binciko bayanai ta cikin Internet. A wajen nemo abu acikin Internet ana amfani da wasu abubuwa guda biyu wadanda ake kira:-

Directories   da  Search Engines.

Shi  Directoies ana amfani dashi wurin nemo wani abu kebantacce, misali abun yashafi magana ne ta Doctors, ko Computer Programmers, ko Engioneer, da sauransu, to idan ain dazaka nemo ya danganta da misalansu ne kamar yadda nakawo, to zakayi amfani da DIRECTORIES wurin nemo bayanan ka, misalan adireshin DIRECTORIES kuwa sune:-

www.searchsystem.com www.directories.goole.com  www.dir.yahoo.com .idan kanason cikakken bayani gameda DIRECTORIES dakuma jerin sunayen Adireshin su saika  (send).

Yanzu kuma zanyi bayani a kan Search Engines.

Da farko Idan zaka binciko bayani ta cikin Internet zaka iya iya nemo bayanin da hausa I dan abin yashafi hausa, sanan zaka iya nemo shi da turanci, misali zaka iya tambayar “Labarun BBC hausa” akawo maka bayani akan Labarun BBC din.

 

MENENE MISALIN ABUBUWAN DA ZAKA IYA NEMOWA A INTERNET

……………………………………

 

MENE SEARCH ENGINES?

Search Engines wasu Websites ne wadanda wadanda ananne zaka rubuta abin da kake nema, sai su binciko makashi, yawanci idan ka budo search engines zaka ga akwai wani dogon layi wanda acikin layinne zaka rubuta abin da kake nema sai ka danna ENTER.

 

ADIRESHIN WASU SEARCH ENGINES

Search Engines da suka fi sanuwa kuma sukafi nemo abubuwa ciki sauri Kadan daga cikin su sune:-

ALTAVISTA = Zanyi bayani akansa nan gaba.

GOOGLE = Shima zanyi bayanin sa nan gaba insha Allahu.

ASKJEEVES = Shi wannan taskar binceken shima yana daga cikin adireshin da zakaje karubuta ain da kake nema, yakawo maka, misali an baku assignment a makaranta anan ne zakaje karubuta abin da aka tambayeku ya baka amsar abin, in kana son cikakken bayani akan sauran websites din da zakaje karubuta assigment a kawo maka amsa karubu wasika zuwa (send).

 

WASU MANYAN SEARCH ENGINES

Su wadannan search engines su ake kira meta search engines, su idan kasa su nemoma wani bayani, suma zasu sa sauran manyan search engines su nemo musu sai sukawo maka abin da kowane search engines ya nemo, ka dan daga cikin su kuwa sune:-

http://www.metacrawler.com

http://www.metasearch.com

http://www.dogpile.com

Idan kanason gabadayansu karubuto (send).

 

YADDA ZAKA BINCIKO WANI BAYANI A GOOGLE

Idan zaka budo Google, zaka zo kusada inda akarubuta Address sai karubuta www.google.com sai kadanna Go ko kadannna ENTER, bayan kadanna zai budo maka feji kamar haka:-

=mfig06=

A wanan dogon layi dakagani ananne zaka rubuta duk abin dakake nema,byayan karubuta abin dakake nema sai kadanna ENTER. Misali kana neman Labaran Hausa ne a Internet, bayan kabudo google sai kazo dogon layin nan kayi click sai karubuta “labaran hausa” bayan karubuta sai kayi click akan Google search, ko ka danna ENTER, bayan kayi click sai kajira yabudo maka result din, idan yabudo maka zakaga website  dabam-dabam, to anan sai karinka karanta kanun bayanan, idan kaga irin bayanin dakake nema sai kayi click akan tushen labarin (inda kaga anja layi), ko kayi click a inda kaga anrubuta Catched, bayan ka danna zai kawo maka websites din dasuke dauke da labaran hausa, anan sai kazabi inda kake so kaje, idan kaje kaga ba irin bayanan dakakeso bane sai kadanna Back zaka gansi acan sama bangaren hagu, idan ka danna zai dawo dakai baya, sai kasake zaban inda zaka sai kayi click. Lokacin daka sa goole yanemo ma abu zaka ga y kawo maka result kamar haka:-

=mfig10=

Amfani da alamar       =sai kuma abu na biyu lokacin dakayi wancan search in zai iya kawo maka website din da akayi magana akan labrun daga baya kuma akayi magana akan hausa, to saboda magance irin wannan matsalar zka iya amfani da wadannan alamun “  “ , yanda zakayi shine kafin karubuta abin dakake nema sai kafara dannan wanan alamar (    ), (yadda ake dannata shine zaka danne SHIFT sai kadanna alamar tana nan kusa da Enter), (kamar haka “labaran safe” ), bayan karubuta abin dakake nema sai kasake danna ta, bayan kagama sai kadanna ENTER, zai kawo maka fejinan da asali akayi magana akan “labaran safe” . Abin dazaka lura anan shine, misali kana neman inda akayi maganar mannir ahmad ne a internt, idan kaje google karubuta mannir ahmad baka sa wannan alamun ba to zai kawo maka websites da akayi magana akan mannir daga baya kuma akayi magana akan ahmad, amma idan kasa wannan alamun zai kawo ma asali inda akayi ayi magana akan “mannir ahmad”. Binciken abu a internet yana bukatar sanin ka’idojin bincike domin sai kaje kata bata lokaci baka samu takamaimai abin dakake nema ba, domin Karin bayani gameda yadda ake nemo abubuwa ta internet ka (send).

 

YADDA ZAKA NEMO HOTO A GOOGLE

Idan hotuna kakeson kanemo,kamar hotunan handsets ko na gidaje kowane irin hoto dai, farko bayan ka budo google.com, idan kaduba saman dogon layin zaka ga inda aka rubuta Images sai kayi click din wurin bayan kayi click din, misali kanason hadset na Samsung, sai kaje kayi click akan dogon layin, sai karubuta Samsung mobiles  kana rubutawa sai kayi click akan search, ko kadanna ENTER, zakaga an kawo maka hotunan handsets din Samsung iri-iri, to misali ace kanason kasiya handset din ne, kana son kasan kudin handset din idan kazo zaka rubuta “Samsung mobiles”+price sai kadanna ENTER, idan aka kawo maka hotunan sai kazabi iri wacce kakeso sai kayi click, za’a kaika inda aka fani farashinata. Misali kanason kasiya nokia 6600 ne zaka rubuta haka:- nokia mobile+6600+price+Nigeria idan karubuta sai kadanna ENTER, zakaga ankawo maka hoton handset din sai kayi click akan Handset din zaka, zaikai ka inda akafadi farashin handset in a Nigeria. Idan kanason cikakkaen bayani gameda yadda ake searchin din image (send).

 

YADDA ZA’A NEMO ABU A ALTAVISTA

Itama Altavisat tana aikine kamar na google amma ta wani wurin tafi google amfani, amfanin kuwa shine misali kanason akawo maka gaba daya websites din da MTN take dasu a internet to zakayi amfani da Altavista ne, farko abin dazakayi zakazo gurin Address in nan sai ka rubuta www.altavista.com  bayan karubuta sai kadanna ENTER bayan anbudo maka fejin akasan layi zakaga inda akarubuta Worldwide sai kayi click din wani box kusada wurin sannan kayi click din cikin layin sai karubuta host:mtnonline.com bayan karubuta sai kadanna ENTER, zakaga ankawo maka gabadaya websites din MTN, idan kuma kanason websites din MTN dasuka yi magana akan GPRS sai karubuta  host:mtnonline gprs za’a kawo maka websites in MTN dasukayi magana akan gprs.

NB=IDAN KANASON CIKAKEN BAYANI GAMEDA YADDA AKE NEMO ABUBUWA A INTERNET KA AIKA DA SAKO ZUWA:- manniruahmad@yahoo.com ko (send).

 

 

P8=WAP

YADDA ZAKA SHIGA YANAR GIZO-GIZO TA CIKIN WAYAR TAFI DA GIDANKA

( how to Browse on your mobile phone)

Zaka iya shiga Internet ta cikin  wayar tafidagidanka (handset), zaka iya binciko bayanai, zaka iya siga E-Mail dinka, zaka iya yin CHATTING, zaka iyayin Dowloading din game, da sauran abubuwa da daama. Duk handsets din da kaga tana da daya daga cikin wadannan :- gprs, wap, wap browser, www service, internet, to wannan Handset din zaka iya browsing da ita. Da farko kafin kafara browsing a handset dinka sai kayi abubuwa guda biyu, farko sai network din da kake amfani adshi sun yi activate din layinka, kuma ka seta handset naka (zanyi bayanin yadda akeyi nan gaba).

 

ME AKE NUFI DA “WAP”  “GPRS”  “CSD”

·          WAP (Wareless Application Protocol), ita kamar software ce da zata iya baka damar ganin abubuwan da suke internet ta cikin handset dinka, kamar Internet Explorer ne a computer, idan baka da web browser (Internet Explorer) bazaka iya ganin shafuffukan da suke cikin Internet ba, to haka ma wap browser take.

·          GPRS (General Packages Radio Service) shi kuma tananne za’a yi connectin handset dinka zuwa Internet, bayan GPRS akwai wasu hanyoyi da za’a iya connecting dinka da internet, don haka kafin kafara yin browsing sai anyi activate din GPRS alayinka tukun.

CSD(Circuit Switch Data) kamar gprs ne ana connecting dinka ta data ne……………………………………………

TA YAYA ZAKAYI ACTIVATE DIN WAP/GPRS A HANDSET DINKA

Kamar yadda nayi bayani da farko cewa:- kafin kafara browsing a handset dinka  sai kayi abubuwa guda biyu, na farko shine sai kayi activate din GPRS a layinka, na biyu sai kaseta wap acikin handset dinka, idan kana son kayi activate din layinka abune mai sauki, zakakira CUSTOMER CARE na layinla sai kace musu “ I want activate wap gprs”, zasu yi maka bayanin yadda zakayi.

 

IN KANA DA LAYIN MTEL

Idan kana da layin mtel kanason ayi activate din WAP/GPRS, zaka kira Customer care ne kamar yadda nayi bayani a baya, sai kace musu “I want activate gprs”.

 

IN KANA DA LAYIN VMOBILE

I dan kana da layin VMOBILE kanason kayi activate wap, abin da zakayi shine, zakayi masu message ne sai kayi send, zasu aiko maka da message din ta OTA (Over The Air ), wato zasu aiko ma da setting din komai, idan sun aiko maka sai kayi save din abinda suka aiko maka,  Abin da zaka rubuta shine:-

Idan Handset dinka bata da camera, kuma kana zaunane a Lagos zaka rubuta masu message, abin da zaka rubuta kuwa shine:-  wapgprs kayi send zuwa 184, idan kuma handset dinka tana camera, zaka rubuta  wapgprs2 kayi sned zuwa 184,

Idan kuma ba acikin garin Lagos kake ba zaka rubuta  wapcsd2 kayi send zuwa 184 idan Handset dinka tana da camera, Idan kuma bata da camera zaka rubuta  wapcsd  kayi send zuwa 184, idan kuma setting mms kakesonyi shima zakayi kamar sauran ne amma shi zakarubuta mms a inda karubuta wap, misali:-   mmscsd2,  Idan kayi haka basu aiko maka da komai ba sai ka kirasu a customer care.

……………………………………

 

 

 

IN KANA DA LAYIN GLO

Idan kana da layin GLO kanason kayi activate din GPRS a handset dinka, abin da zakayi shine zaka rubuta message sai ka aika masu zasu aiko maka da setting din, abin da zaka rubuta shine:-  activate wap  <kamfanin handset dinka>  <model din handset dinka> sai kayi send zuwa 927, misali:-  activate wap nokia 6600 kayi send zuwa 927. in kuma mms ne zaka ……………………… idan kuma ka aika basu aiko maka da komai ba har bayan kwana uku sai ka kirasu a CUSTOMER CARE 121 kace “I want to activate wap”.

………………………………….

 

IN KANA DA LAYIN MTN

In kana da layin MTN kanason kayi activate din “MTN WAP” shima zakarubuta message ne zaka rubuta:-   settings kayi send zuwa 3888 in ka aika basu aiko maka da komai ba har bayan kwana 1, sai kasake rubuta settings amma shi zakayi send zuwa 4777, idan duk kayi haka basu aiko mada komai ba sai kakira shu a CUSTOMER CARE 180 sai kace masu “I want activate mtn wap/gprs” zasu yi ma bayanin yadda zakayi.

 

IDAN KANA DA NOKIA, SONY ERICSSON, SIEMENS, KO MOTOROLA,  KA (SEND), IN SHA ALLAHU ZAN AIKOMAKA DA SETTING TA CIKIN OTA(OVER THE AIR).

 

 

WADANNE IRIN ABUBUWA MUTUM ZAI IYAYI IDAN MUTUM YA SETA HADSET DINSA TANA WAP/GPRS

Others

My About page is also a great place to give information about others involved with my site's topic, such as the leaders of my organization, club, or company; an ancestor; my family; and so forth.

IDAN KANA SON CIKAKKEN BAYANI

Links to Other Sites